ABIN TAKAICI, KALLI MAKUDAN KUDADEN DA GOMNATI KE KASHEWA WAJAN SHIGO DA MAN FETIR NIGERIA

 


Gwamnatin Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ta kashe sama da Naira tiriliyan 16.9 wajen shigo da lita miliyan dubu dari 132 da doriya na man fetur daga kasar waje zuwa Najeriya.


Alkaluman da aka samu daga Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna cewar Kamfanin Man Fetur na Kasa ya dogara ne da man fetur din da ake shigo dashi daga kasashen ketare.


Hakan ya faru ne saboda halin da matatun man man fetur na kasar nan suka kasance tsawon shekaru,duk da cewar gwamnati na gyara matatun Port Harcourt da Warri, da aka ware kusan dalar Amurka miliyan dubu 2 da Dala miliyan dari 9


A ganinku cigaba da shigo da man fetur kokuma gyara namu matatun wanne ne mafita?


SOURCE :Rahama Tv on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments