2023: Zan ɗora a kan nasarorin Buhari -- Tinubu

 Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Tinubu, ya ce zai dora kan nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata.


Tinubu ya bayyana haka ne a yau Talata a Jos a wurin ƙaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na 2023.


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana cewa Buhari ya taka rawar gani a fannin samar da ababen more rayuwa tare da kafa ginshikin bunkasa noma da sauran fannoni.


“Ba mu da kwanciyar hankali, sai mu ka koma ga Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya kuma fara farfadowa da kwato Najeriya.


“Ya fara ne da lalata tutocin ƴan ta’adda abisa tsari, dabara da kuma hikima, kuma a yau babu wata tuta a kananan hukumominmu a Nijeriya.


“Najeriya ta fara nutsewa amma sai Buhari ya tsamo mu ya kuma ce Najeriya ba za ta nutse ba a zamaninsa da kuma lokacin APC,” inji shi.


Ya bayyana cewa Buhari ne ya jagoranci gudanar da zaben fidda-gwani na gaskiya da inganci wanda ya samar da shi a matsayin mai rike da tuta.


SOURCE :  DAILY NIGERIAN HAUSA ON FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments