--
Ba a taɓa Gwamnatin da ta kai ta Buhari cin hanci da rashawa ba — Hajiya Naja'atu

Ba a taɓa Gwamnatin da ta kai ta Buhari cin hanci da rashawa ba — Hajiya Naja'atu

>


 


Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame .


Mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar da ‘Yan Sanda, PSC, Naja’atu Mohammed ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo Hakan ya biyo bayan yadda ya yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye da Jolly Nyame na Jihar Filato da Taraba a makon da ya gabata Kamar yadda Mrs Mohammed ta ce yayin da RFI ta tattauna da ita, ya kamata Buhari ya gane cewa dukiyar Najeriya ba tashi ba ce 


Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba. Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan 


Ba Bu Gwamnatin Da Ta Fi Ta Buhari Rashawa: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame.


An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020. 


A wata tattaunawa da Radio France International, RFI a ranar Litinin, wacce Daily Nigerian ta saurara, Mrs Mohammed ta ce ya dace Buhari ya gane cewa dukiyar Najeriya ba ta shi bace. A jiharsu ya dace a yafe musu in ji Mrs Mohammed A cewarta, ya kamata gwamnonin jihohinsu su yafe musu ne, saboda acan suka aikata rashawar, don kundin tsarin mulki ya bayar da yafiya ne ga jihohin da aka aikata laifuka. 


Ta kara da cewa yafe wa tsofaffin gwamnonin yana nuna cewa ba a shirya kawo karshen rashawar Najeriya ba. Ta ce kotu ta tabbatar da zargin da ake musu don haka yafiyar na nuna cewa ba a yaki da rashawa a kasar nan. 


A cewarta: “Gwamnati ta yi kuskure. Ya dace shugaban kasa ya gane cewa dukiyar al’umma ba ta shi bace. Gwamnatin tarayya ba ta da damar yafe wa wadanda suka tafka laifi a jihohinsu. “Abu na biyu shi ne wannan yafiyar ta Buhari tana nuna cewa gwamnati ta gaza. Wannan shiyasa muke fama da rashin tsaro. 


Satar biloniyoyin Filato wacce kotu ta tabbatar, ba za ta rasa alaka da kashe-kashe, tabarbarewar ilimin jihar, lalacewar titina da kashe-kashen da jihar take fama da shi ba. “Bayan EFCC da kotu sun gama iyakar kokarinsu tsawon shekaru, bai dace kawai ka yafe wa masu laifin ba. Ba kudinka suka sata ba. Me yasa gwamnatin Buhari ta ke yin yadda ta ga dama?” 


Ta ce a Tarihin Najeriya ba a taba mulki mai rashawa da sata kamar na mulkin Buhari ba A cewarta kundin tsarin mulki bai bayar da damar yin wannan haukar ba. Idan haka ne ya kamata a yafe wa ‘yan ta’adda. Saboda babu ta’addancin da ya zarce satar da gwamnonin suka yi. Ta ci gaba da cewa an zabi Buhari ne don ya yi yaki da rashawa, amma yanzu shi ne ya ke yafe wa masu rashawar. Alamu na nuna cewa Buhari ba abin amincewa bane, in ji ta. Ta ce a tarihi ba a taba gwamnatin da ta fi ta Buhari rashawa ba a kasar nan. Satar da ake yi ta zarce tunan.

0 Response to "Ba a taɓa Gwamnatin da ta kai ta Buhari cin hanci da rashawa ba — Hajiya Naja'atu"

Post a Comment