--
Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci

Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci

>

Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci
 

Babban limanin masallacin Apo Legislative Quarters Mosque, Shiekh Nuru Khalid, wanda aka dakatar kan wa'azin da ya yi da ake yi wa kallon na 'sukar gwamnati' ya yi magana a karon farko, rahoton The Punch.


Khalid, wanda aka fi sani da Digital Imam, a cikin wani sako da ya wallafa cikin harshen larabci ya ce, "Allah ne mafi girma da buwaya. Shi ya ke bada mulki kuma ya karba daga hannun duk wanda ya ga dama lokacin da ya ga dama."


Wannan sakon ya yi kamanceceniya da sakon da ke cikin wasikar da Sanusi Lamido II ya rubuta lokacin da aka tube shi a matsayin sarkin Kano.Babban malamin ya kuma bukaci yan Najeriya su cigaba da yi wa kasarsu da shugabanni addu'a. Ya ce, "Ya Allah! mai girma da buwaya, kai kake bada mulki ga wanda ka ke so, kuma ka kwace daga wanda ka ke so, ka ke daukaka wanda ka ke so kuma ka kaskantar da wanda ka ga dama, dukkan alheri na hannun ka, lallai kai ke da iko a kan komai." A ranar 1 ga waan Afrilu ne kwamtin masallacin Apo Legislative Quarters ta dakatar da Khalid bisa wa'azin da ya yi a ranar Juma'a.


A cikin wa'azin, Khalid ya caccaki gwamnati kan gazawarta wurin samar da tsaro a kasar nan. Malamin ya fada wa masu zabe kada su zabi duk wani dan siyasa da ba zai iya tabbatar musu da tsaron rayuka da dukiyoyinsu ba.

0 Response to "Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci"

Post a Comment