--
N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

>

 N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

Kimanin matasan Najeriya milyan shida da rabi suka nemi aikin N-Power zango na uku na gwamnatin tarayya Ministar harkokin jin kai da jin dadin al'umma,

Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana haka A cewarsa kawo yanzu mutum 510,000 aka dauka kuma za'a dauki karin sabbin mutane 490,000

Ministar harkokin jin kai da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa kimanin yan Najeriya milyan shida da rabi suka nemi zango na uku na shirin aikin N-Power. 

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar matasa aikin wucin gadi na N-Power ne a shekarar 2016.

Shirin na baiwa matasa aikin koyarwa ko noma tsawon shekaru biyu kafin a yaye su. Kawo yanzu, an yaye wadanda sukayi musharaka a zango na daya A da zango na biyu B.

Hajiya Farouq ta bayyana adadin wadanda suka nemi na zango na uku ne a taron kaddamar da tsarin kula da yan gudun hijra a Abuja, rahoton Punch. Farouq yace: "Ma'aikatar ta samu nasarar yaye mutum 500,000 na zangon A da B a 2020 kuma mutum milyan 6.4 sun nemi zangon C. 

"Karkashin zango na uku C dibar farko, an dauki mutum 510,000 kuma suna amfana yayinda za'a dauki karin mutum 490,000 bisa izinin shugaban kasa na a kara mutum milyan daya."

0 Response to "N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya"

Post a Comment