--
DALILAI 10 DA SUKE NUNA OSINBAJO ZAI IYA SANADIN FADAN ADDINAI

DALILAI 10 DA SUKE NUNA OSINBAJO ZAI IYA SANADIN FADAN ADDINAI

>


 DALILAI 10 DA SUKE NUNA OSINBAJO ZAI IYA SANADIN FADAN ADDINAI


DAGA Farooq Kperogi


1. Wasikar da Chochin RCCG ta aikewa sauran Chochi Chochi tana neman dasu shiga siyasa dumu dumu, ya faru ne dalilin Osinbajo, kuma yayi daidai da abinda aka sanshi dashi na siyasar bangaranchi ta addini.


Misali: A 2013 Osinbajo ya kafa Kungiyar Christian Conscience Group tare da Enoch Ajiboso, Dele Sobawole da Babban Rabaran Joseph Ajayi domin dabbaka da'awar samun Gwamna Kirista a Jahar Lagos.


2. Dabbaka da'awar samun Kirista Gwamna a Lagos da Osibanjo yayi, ba don neman daidaito bane, saboda musulmi bai taba Gwamna a Ondo da Ekiti ba. Domin ko a Jahar sa ta Ogun Ibikunle Amosun ne Gwamna musulmi na farko da aka taba zaba tun 1979, duk da kuwa yawan musulmai akalla yakai kashi 50, amma Osinbajo bai damu da wannan ba.


3.Hanyar da Osinbajo yayi amfani da'ita wajen kawo takaddamar addini gabanin zaben 2015, itache hanyar da yake amfani da'ita yanzu. Wasikar Chochin RCCG data fito kadanne daga chikin hanyoyin tada rigimar addinai.


4. Osinbajo mutum ne mai tsananin kiyayya ga musulunchi, yana rufe kiyayyar sa da dadin baki kuma yana tarayya da musulmai ne kawai don chimma burinsa na siyasa. Yana shiga masallatai da takalmi da nuna rashin girmamawa ga wuraren ibadun su.


5. Osinbajo yana kallon musulmai ne a matsayin wadanda suke batattu suke bukatar  shiriya ko kuma a kautar dasu ta kowanne hali.

Misalin wanan kuwa shine; a 22, 2022 kamar yanda Jaridar Sunshine Truth ta wallafa, a yayin jana'izar  Mahaifiyar Gwamnan Ondo Olusegun Mimiko, Osinbajo da aniya, yache Mama Muinat Mosekonla Mimiko ta fita a addinin musulunchi gabanin karshen rayuwar ta. Duk da maganar sa karyane, wannan bai kamata ba kuma ya sosa rayukan musulmai.


6. Yarabawa musulmai suna chewa, akwai 'ka'ida a kamfanin Osinbajo Simmons Cooper Partners, da ta tsaya akan chewa, kashi 99 na ma'aikata dole su zama Kiristochi.


7. Chochin Pentecostal suna so Osinbajo ya zama Shugaban Kasa domin su gaskata chewa busharar Pastor Enoch ta chewa dayansu zai zama Shugaban kasa a lokachin rayuwar sa ta tabbata. Za'ayi amfani da wannan wajen samarwa Osinbajo masoya musamman a Kasar yarabawa.

Wannan yanada illa, domin zai saka kiristochi da basa wannan darika ta Osinbajo su yaki abin, kuma zai saka Musulmai a arewa, musamman wahabiyawa sufara neman kujerun siyasa ido rufe don ganin sun yaki Pentecostals, daganan za'a shiga halin tsammanin yakin addinai a Najeriya.


8. Irin salon Osinbajo abune da ba'a taba gani ba a Najeriya, mafi yawan 'yan siyasa suna amfani da addini ne domin su samu mulki, shikuwa Osinbajo yanason amfani da mulki ne domin karfafa Darikar addinin sa, wanda hakan zai jawo babbar rigimar addinai achikin kasa.


9. A kasidar dana gabatar a baya, na kira Osinbajo a matsayin 'gidan Ashana' wanda haduwar sa da Musulmi a matsayin ashana, zai janyo babbar hatsaniyar addinai. A zahiri yawuche haka. Shi tartashin wuta ne.

A kasidar Nuwamba 10, 2019, wanda na yiwa take da "The Trials of Brother Osinbajo" mai kasida a Jaridar Nigerian Tribune Festus Adedayo ya bayyana yanda, lokachin da Buhari yake jinya a Landan, Osinbajo ya halarchi taron addu'a a Chochin RCCG dake Jahar sa ta Ogun, yanda wani Fasto yayi addu'ar Buhari ya mutu, domin Osinbajo ya zama Shugaban Kasa, wanda hardashi Mataimakin Shugaban Kasa akayi kuwwar Ameen, wanda daga baya Osinbajo ya umarchi hadimin sa daya karyata faruwar wannan al'amari.

Kamar yanda wani masani mai suna Otto von Bismarck yake fada " Kada ka yarda da komai a siyasa, harsai a hukumanche an karyata shi." Ni kuwa, satin daya wuche wani abokina Dan yankin su Osinbajo ya tabbatar min da faruwar al'amarin.


10. Duk da yana auren Jikar Marigayi Chief Obafemi Awolowo kuma sunfito daga gari daya; Osinbajo bai gamsu da hikimar marigayin ba na chewa "Ya kamata a hade siyasa da addini."

Duk da kuwa dukkan daukaka da Osinbajo ya samu ta dalilin Musulmai ne, amma mutum ne mai tsananin kiyayya a garesu.


Rikichin addini abu ne mai illa, kasashe kadanne suke iya tsira daga gareshi. Kada kuche ban gargade ku ba!


Fassarawa Mansur Aliyu Saeed

0 Response to "DALILAI 10 DA SUKE NUNA OSINBAJO ZAI IYA SANADIN FADAN ADDINAI"

Post a Comment