--
Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

>

 


Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

Kungiyar Izalah ta bude sabon ginin Masallaci a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron a matsayin babban bako Shugaban kungiyar, Imam Abdullahi Bala Lau, ya yi addu'an zaman lafiya ga Nigeria 


Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bude sabon Masallacin da kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS ta gina a birnin tarayya Abuja.


An bude Masallacin ne yau Juma'a, 25 ga Maris, 2022.


Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a taron bude Masallacin. Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan; Kwamishanan ilimi na biyu na jihar Kano, Alaramma Ahmed Sulaiman, dss.


Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar JIBWIS za ta bude sabon Masallacin da ta gina a birnin tarayya Abuja ranar Juma'a. 


Jibwis a jawabin da ta saki ranar Talata ta bayyana cewa an gina ne da kudaden fatun layya da mutane ke badawa fisabilillah.


Izalah ta bayyana hotunan Masalaccin dake unguwar Utako, kwaryar garin Abuja.

0 Response to "Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a"

Post a Comment