--
Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara:- Cikakken Bayani

Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara:- Cikakken Bayani

>


 Wata budurwa da ta niƙi gari tun daga Patakwal har Legas ziyartar Saurayi, ta wayi gari bata iya magana Bayanai sun nuna cewa mutanen yankin sun tashi cikin tashin hankali bayan faruwar lamarin ba zato ba tsammani Yan sanda sun kama wanda ake zargi, kuma ya ce ta tashi lafiya ƙalau har magana ta masa


 Mazauna yankin Iyana-Isashi a Legas sun wayi gari da tashin hankali bayan wata kyakkyawar budurwa ta zama Bebiya bayan kai wa Saurayinta da suka haɗu a Facebook ziyara. Vanguard ta rahoto cewa budurwan wacce ta fito daga jihar Benuwai, amma ta na zaune a Patakwal, jihar Ribas ta rasa maganarta ne bayan kwana a jikin saurayinta.

Lamarin ya soma ne daga tashi da safe, bayan Matashiyar ta tashi, ta ɗauki Ruwan Leda kuma ta fita tsakar gida domin goge bakinta.


A wannan lokacin ne ta fahimci ta zama Bebiya, ba zata iya yin magana ba, sai dai Saurayin nata yace lafiya ƙalau suka tashi.


Saurayin ya ce: "Na haɗu da ita a kafar sada zumunta, muka kulla abokantaka kuma muka fara soyayya. Makon da ya gabata ta zo har Legas daga Patakwal domin kawo mun ziyara." "Mun kwashe lokaci tare komai lafiya ƙalau har zuwa safiya lokacin da ta tashi, ta fita goge baki. Ta ɗauki ruwan Leda a jakar "Pure Water' a cikin gidan ta nufi waje, tana gama goge baki ta nemi bakin magana ta rasa." "Na ji tsoro sosai saboda lokacin da ta tashi da safe sai da ta mun magana kafin ta ɗauki ruwan ta fita waje."


Rahotanni sun bayyana cewa bayan jaraba duk wani kokari na dawo mata da magana ya ci tura, mutane sun faɗa wa yan sandan Caji Ofis ɗin Iyana-Isashi domin su kama wanda ake zargi.


Da yake tabbatar da kama mutumin kakakin yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, yace jami'ai sun kama wanda ake zargi amma daga baya suka sake shi bayan iyayen budurwar sun zo. Iyayenta sun kafe cewa a ba su ƴarsu domin su koma da ita gida a jihar Benuwai, su nema mata magani.

"Bayan kwararan shaidu sun tabbatar da cewa iyayen budurwar ne, muka ɗamƙa musu ita a hannun su," inji Kakakin yan sanda.


Domin karin bayani Ku latsa Nan CIKAKKEN LABARIN

0 Response to "Budurwa ta zama Bebiya daga zuwa kaiwa Saurayinta na Facebook Ziyara:- Cikakken Bayani "

Post a Comment