--
Menene E-Naira ? Cikakkun Amsoshin Tambayoyi Da Karin bayani Akan Kudin Internet (e-Naira)

Menene E-Naira ? Cikakkun Amsoshin Tambayoyi Da Karin bayani Akan Kudin Internet (e-Naira)

>


Menene E-Naira ?


E-Naira kudi ne da kimiyya tazo dashi sabanin takarda da tsaba da muka saba amfani dasu kai tsaye daga bankin kasar nan wanda ake kira da CBN ba sauran bankunan Yan kasuwa ba. Zaa iya amfani da e-Naira kamar yanda muke amfani da Kudin takarda da tsaba wajen yin cinikayya da sauran musaya da akeyi da Kudin takarda.


Bambancin e-Naira da Kudin da muke ajiyewa a asusun kasuwanci na ajiyar Kudi Banks other than CBN ?


 Sannan mene amfani ajiye kudi a wallet Din E-Naira?


Na farko dai kudin ka yana kyakykyawan hannu, babu gara  babu zago. E-Naira zata taimaka sosai wajen samawa Kasa kudin shiga. Sannan tsarin yabi doronda kowanne addini kake zaka iya amfani dashi saboda babu ruwa. E-Naira zai taimaka wajen muamala ta kudi ba tare da ganin juna ba, acikin Kasa harma da wajenta.


E-Naira kuɗi ne da baza ka iya riƙewa a hannunka ko kuma aljihunka ba. Sai dai ka mallaka ta hanyar ajiyarta a cikin wani kurtu dake yanar gizo da ake ambata da eWallet mai ɗauke da laƙabin eNaira speed wallet. 


Za ka iya mallakar wannan kurtun ne ta hanyar ziyartar PLAYSTORE domin ka sauke kurtun. Masu amfani iPhone ma za su iya saukewa daga tasu manhajar. 


Ta fuskar tsaro, kurtun yana da buƙatar sai kayi rijista da za ta baka kariya daga farmakin ƴan damfarar yanar gizo. Kurtun na da two-factor verification, ta yadda muddin kaga ka rasa kuɗinka sai dai in sakacinka, kamar dai yadda ka kan iya sakaci da ATM ɗinka.


Sai dai akwai bambanci tsakanin kurtun Ƴan Kasuwa da kuma na saɓanin su. Ƴan kasuwa ina nufin wanda suke da asusun dake ɗauke da rijistar sunan kasuwancin su. eNaira merchant wallet ita ce tasu. Dan haka za su iya sauketa kamar yadda ake sauke kowace irin manhaja daga PLAYSTORE ko makamancin sa, ga masu amfani da iPhone.


Za ka iya dukkan wata hada-hadar kasuwanci da eNaira tamkar yadda kake yi da kuɗaɗen aljihunka ko na asusun ka.


Za kuma ka iya tura eNaira zuwa asusun bankin ka, ko na wanin ka. kana za ka iya tura kuɗin dake cikin asusun ka zuwa eWallet. Haka nan za ka iya tura e-Naira daga eWallet ɗinka zuwa eWallet ɗin wanin ka.


Abu mai muhimmanci a cikin hada-hadar eNaira shi ne, kyauta ake turawa ba tare da an taɓa maka ko sisi ba. Domin eNaira mallakin babban Bankin Ƙasa na CBN ne, dan haka duk wani nauyi dake kan eNaira yana kan CBN. 

0 Response to "Menene E-Naira ? Cikakkun Amsoshin Tambayoyi Da Karin bayani Akan Kudin Internet (e-Naira)"

Post a Comment