--
Yanzu yanzu: IGP Usman ya aika tawagar bincike ta musamman

Yanzu yanzu: IGP Usman ya aika tawagar bincike ta musamman

>

IGP Usman Alkali Baba: Hoto Daga Daily Nigerian


Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin tura tawagar 'yan sanda ta musamman domin ƙaddamar da bincike kan kashe matafiya Musulmai a garin Jos na Jihar Filato.


Wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sanda na ƙasa, Frank Mba, ta ce matakin ya biyo bayan kashe mutum 25 a harin wanda wasu "matasan ƙabilar Irigwe" suka tare matafiya ranar Asabar, inda suka raunata wasu kusan 50.


Sanarwar ta ce DIG Sanusi N. Lemu ne zai jagoranci tawagar sannan kuma za ta ƙunshi jami'ai daga ɓangarorin bincike da dama na rundunar. Kazalika an tura ƙarin jami'an tsaro yankin na Rukuba domin kare sake afkuwar tashin hankalin.


IGP Usman ya ce ya zuwa yanzu an kama mutum 20 da zargin aikata kashe-kashen sannan an ceto mutum 33 da suka ji raunuka yayin harin.


Rahotanni sun ce an tare motocin matafiyan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Jihar Ondo da ke kudancin Najeriya bayan sun halaraci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a Jihar Bauchi.


Source: Bbc Hausa

0 Response to "Yanzu yanzu: IGP Usman ya aika tawagar bincike ta musamman"

Post a Comment