--
Yadda Mai digiri ya ajiye aikin banki ya koma sayar da burodi a titi duba yadda abun ya faru

Yadda Mai digiri ya ajiye aikin banki ya koma sayar da burodi a titi duba yadda abun ya faru

>


Da digirin shi da komai ya koma sayar da burodi akan titi, yanzu haka yana samun naira dubu biyar kowacce rana


Wani ma’aikacin bankin Zenith mai suna Ali Dahiru, ya ajiye aikin bankin ya koma sayar da burodi, ya ce wannan shawara da ya yanke ta zame masa alkhairi sosai.



Dahiru, wanda yake da takardun HND, ya kammala karatu a Polytechnic dake Kaduna, a fannin tattalin arziki, ya sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa yana sayar da burodi akan titiunan Kaduna, kuma yana alfahari da wannan aiki na sa.


Bayan na kammala karatuna, na fara aiki da bankin Zenith na tsawon shekara shida, kafin daga baya na ajiye aikin na fara sayar da burodi.


Da yake bayyana yadda ya fara sha’awar sayar da burodi, Dahiru ya ce wani mutumi da yake kai musu burodi banki suna saya, shine ya sanya masa sha’awar sana’aDahiru

A lokacin da nake hutu ne na yanke shawarar magana da mai sayar da burodin a bankin, inda na nuna masa ina sha’awar sana’ar.


Na gano cewa ribar da yake samu a wata wajen sayar da burodi tafi albashin da nake dauka a wata a banki.


Ya yi kokarin karya mini gwiwa akan cewa a matsayina na mai digiri, sayar da burodi bai dace dani ba, amma naki yadda da maganar shi.


A hankali na bar aikina na fara sayar da burodi akan babur dina, abinda ya bawa mutane da dama mamaki.


Ali Dahiru


Ya ce yanzu ya na samun cigaba sosai, fiye da lokacin da yake aiki a banki, inda ya ce yanzu haka yana iya taimakawa wasu da kudi.


Bana jin kunyar sayar da burodi a matsayina na mai digiri; wadanda suke tinkaho da cewa suna da digiri basa aikin yi yanzu a wajena suke neman taimakon kudi; sune suke jin kunya ba ni ba.


A yanzu haka ina iya ajiye N5,000 a kowacce rana idan nayi sa’a kwastomomina basu rike mini kudi ba, amma idan sun rike wani lokacin ina tashi da naira N3000 kowacce rana.


A cewar sa, matsalar kawai da yake samu ita ce hanyar kaiwa kwastomominsa burodi, inda yace yanzu babur da yake amfani dashi ya yi kadan wajen daukar kaya.


Ina amfani da babur ne yanzu, kuma bana iya daukar burodi da yawa da zai ishi duka mutanen da suke sayen burodi a wajena; wani lokacin ina zuwa wajen sayen burodin sau uku sau hudu a rana, wani lokacin ma kafin na tashi daga aiki burodin yana karewa a wajen da nake zuwa ina saya.


A karshe ya yi kira ga masu digiri da basu yin aiki su rungumi sana’a duk kankantar ta.


Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.


Source: NAN

0 Response to "Yadda Mai digiri ya ajiye aikin banki ya koma sayar da burodi a titi duba yadda abun ya faru"

Post a Comment