--
Tirkashi: Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

Tirkashi: Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

>


A Jihar Rivers - Wani mutumi, Bright Ben, ya zargi babban faston cocin su ta General Overseer dake Eneka, karamar hukumar Obio-Akpor, jihar Rivers da yi masa kwacen mata, kamar yadda punch ta ruwaito. 


Bright ya bayyana cewa lamarin ya fara ne daga lokacin da aka aka baiwa matarsa da suke shekara 12 tare mukamin mai hidima ga coci. 


Yace tun daga wannan lokacin matarsa mai suna Tina, ta tatttara kaya ta bar gidansu tare da 'ya'yan da suka haifa guda biyu.


 Sai da na nemi shawarar Faston kan ɓatar matata Bright yace ya jima yana neman inda matarsa ta koma kuma sai da ya kira faston nasa domin neman shawara kan lamarin. 


Ya kara da cewa daga baya sai ya gano inda ya koma ranar Lahadi yayin da yaga kyawawan hotunanta ta sake wani auren na daban. 


Shin wannan abun kunya ne? Bright, a wani rubutun takaici da yayi a shafinsa na Facebook, yace wannan auren na malaminsa da matarsa babban abun kunya ne. A rubutunsa, 


Bright yace: 


"Malamin coci na ya auri matata. Mun kasance ma'aurata da Tina shekaru 12 da duka gabata. Na gabatar da uta faston nawa daga nan muka cigaɓa da halartar cocin tare." 


"Ba da jimawa ba a ka baiwa matata mukamin mataimakiya a cocin watanni 7 da duka shuɗe, watarana kawai sai tattara kayan tabar gidana lokacin ina wurin aiki.


"Na neme ta a ko ina kuma na kira duk wanda ya dace har da faston cocin namu domin shike maganin matsalolina. Amma bayan wani lokaci sai ya daina daga kiran wayata." 


"Na jima ina nemanta har sai da na ga hotunanta akafar sada zumunta, faston ya yi ikirarin ubangiji ne ya faɗa masa cewa matarsa ce." 


Tina ta maida martani ga Bright A martani da ta yi a kafar sada zumunta, Tina, ta bayyana cewa da fece ta bar mijinta ne saboda cin zarafinta da yake yi da kuma rashin kulawa. 


A rubutun ta Tina tace: "Tsohon mijina yaso maida ni matar banza a kafar sada zumunta, lokacin da muke tare yasa na viyo bashi wanda har yanzun ban kammala biya ba.


" "Ya hana ni cika burina na zama mawakiya, kai daga baya ma ya faɗamun cewa babu aure tsakanin mu, ina zaune ne kawai domin kula masa da ƴaƴan mu." 


"Yayi alkawarin lalata rayuwata, amma yanzun yazo kafar sada zumunta yana kokarin ɓata wa wani suna. Nima lokacina na ne nayi abinda raina ke so."


 Tina ta kara da cewa karya yake yace baisan inda nake ba domin na bar gidan shi ne bayan ya kulle ni a ɗaki ya tafi da makullan.


 Bright bai biya sadakin Tina ba 


Mahaifiyar Tina,Christiana Everest, ta bayyana cewa mijin diyarta na farko bai biya sadakin auren su ba har yanzun. Ta bayyana cewa Bright ya baiwa kowa hakkinsa maza da mata na iyalan gidan mu amma banda iyayen Tina. 


Tace duk lokacin da aka ce masa ya kai wa iyayen amaryar tasa ziyarsa sai yace ba yanzun ba zai je daga baya. Dagaske zargin da ake maka ka aikata? Bright a ya musanta duk wasu zarge-zarge na cin mutuncin matarsa da aka ɗira masa. 


Hakazalika ya musanta zargin da mahaifiyar tsohuwar matar tasa ta masa cewa bai biya sadaki ba, iɓda ya kara da cewa ya yi komai lokacin bikin al'ada. 

0 Response to "Tirkashi: Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure"

Post a Comment