--
Sabon tsarin bada rancen kudi domin bunkasa kasuwanci wanda babu kudin ruwa aciki kowa yaje ya cike

Sabon tsarin bada rancen kudi domin bunkasa kasuwanci wanda babu kudin ruwa aciki kowa yaje ya cike

>

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari (GCFR), ta hannun ƙaramin bankin harkokin kasuwanci, (NIRSAL), ƙarƙashin babban bankin ƙasa (CBN), za ta sake rabawa ƴan Nageriya tallafin bashi wanda babu kuɗin ruwa a ciki.

Duk mai sha'awar bashin zai iya ziyartar wannan adireshi na: www.nmfb.com.ng domin ya cike buƙatarsa ta neman tallafin bashin.

Sharaɗi ne ga duk masu kamfanoni da za su nemi wannan bashi sai su na da takardun harkokin kasuwanci da kuma bayanai akan yadda annobar (Covid-19) ta shafi harkokinsu. Sannan kuma masu kasuwanci na kai a gida za su iya nema ba tare da wannan sharaɗin ba.

Adadin kuɗin da kowane mai kamfani zai iya neman rancen shi ne Naira Miliyan 2,500,000, masu kasuwanci a gida kuma Naira 1,000,000.

Duk mai sha'awa zai iya cikewa ta wannan adireshi na: www.nmfb.com.ng
ko ya tuntuɓe su a lambar wayarsu: 09010026900. 

Nirsal Microfinance Bank 


0 Response to "Sabon tsarin bada rancen kudi domin bunkasa kasuwanci wanda babu kudin ruwa aciki kowa yaje ya cike"

Post a Comment