--
Kalli Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure

Kalli Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure

>


Kyawawan hotunan 'ya'ya matan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Halima, Zahra da Hanan tare da mazansu na aure yayin liyafar cin abincin rana ta bikin dan uwansu, Yusuf Muhammadu Buhari sun bayyana.


An yi kasaitacciyar liyafar, wacce ta hada manyan mutane a ranar Lahadi, 22 ga watan Augusta a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa ta Aso Villa. 


'Ya'yan shugaban kasan mata sun karkace tare da daukar kyawawan hotuna da mazansu na aure yayin da ake liyafar cin abincin ranan.


An ga Halima Muhammadu Buhari tare da maigidanta, Mohammed Sheriff 



Wannan Itace Halima Buhari da mijinta, Mohammed Sheriff. Hoto daga @thebeginningofyz Source: Instagram 


Ba a bar 'yar kwalisa Zahra Muhammadu Buhari a baya ba, hoton ta ya bayyana tare da maigidanta Ahmed Indimi a wurin liyafar. 



Wannan Itace Zahra Buhari tare da mijinta Ahmed Indimi. Hoto daga @thebeginningofyz Source: Instagram 


Aisha Hanan Buhari da kanta ta dauka kyakyawan hoto tare da mijinta Muhammad Turad Sha'aban a wurin liyafarInstagram




Wannan itace Hanan Buhari da mijinta Muhammad Turad Sha'aban. Hoto daga @thebeginningofyz Source: Instagram 


Source: Legit.ng 

0 Response to "Kalli Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure "

Post a Comment