--
Kalli Hoton 'Yan Boko Haram Su 19 da suka mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno

Kalli Hoton 'Yan Boko Haram Su 19 da suka mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno

>


An samu sabon nasara a yaki da yan ta'adda yayinda wasu yan Boko Haram/ISWAP suka mika wuya ga rundunar FOB dake Bama, jihar Borno. 


A jawabin da Diraktan yada labarai na hukumar Soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya saki ranar Laraba, 4 ga Agusta, yace mayaka 14 tare da iyalansu suka mika wuya.


Nwachukwu ya ce Sojojin sun karbi tubabbun yan ta'addan ne a cikin dajin Sambisa ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta. 


Yace: 


"Yan ta'addan sun hada da maza mayaka 19, mata 19 da yara 49 yan garin Njimia kuma sun ajiye makamansu." "Yan ta'addan da iyalansu yanzu haka na hannun jami'ai don gudanar da bincike kansu, yayinda aka yiwa yaran rigakafin shan inna." 


Shugaban Sojin kasa, Faruk Yahaya, ya jinjinawa Sojoji bisa wannan nasara da suka samu. 


Source: Legit.ng News 

0 Response to "Kalli Hoton 'Yan Boko Haram Su 19 da suka mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno"

Post a Comment