--
Gwamnatin Jihar katsina tabawa mutane umarnin Mallakar Bindiga Duba dalili>>>

Gwamnatin Jihar katsina tabawa mutane umarnin Mallakar Bindiga Duba dalili>>>

>


Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi kira ga mutanen da ke zaune a yankunan da ke da yawan 'yan bindiga da su mallaki makamai su kare kansu daga ta'addanci. 


Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na yada labarai ga gwamnan, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, wanda Daily Trust ta samu. 


Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su mika wuya ga 'yan bindiga ba tare da wani yunkuri na kare kansu ba, lura da cewa tsaro aikin kowa ne. 


Channels Tv ta ruwaito gwamnan na cewa: 


Meye gwamnati ke yi game da mutuwar mutane 10 sanadiyyar jami'an kwastam?


Jaridar Legit Hausa ta gano Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a garin Jibia ranar Talata 17 ga watan Agusta, lokacin da ya kai ziyarar jajantawa kan rasuwar mutane 10 da wasu jami’in hukumar kwastam ta Najeriya suka yi sanadiyya a ranar Litinin yayin tuki a kan aiki. 


Da yake magana game da mutuwar mutanen 10, Gwamna Masari ya tabbatar wa mutane cewa gwamnati tana bin dukkan matakan da suka dace na shari’a don neman hakkin iyalan mamatan, da kuma wadanda suka sami raunuka daban-daban. 

0 Response to "Gwamnatin Jihar katsina tabawa mutane umarnin Mallakar Bindiga Duba dalili>>>"

Post a Comment