--
Duba yadda Darajar Naira ta qara sauka kasa, Yanzu farashin Dalar Amurka $1 yakai N515 a kasuwa,

Duba yadda Darajar Naira ta qara sauka kasa, Yanzu farashin Dalar Amurka $1 yakai N515 a kasuwa,

>


Najeriya - A ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, 2021, kudin Najeriya na Naira ya rasa kimar da ya samu a kan Dalar Amurka a cikin ‘yan kwanakin nan.


Nawa ne farashin Dala a yau? Jaridar Punch ta ce yayin da ake fama da karancin kudin kasar waje a halin yanzu, darajar Naira ya ragu a kasuwar canji a cikin tsakiyar wannan makon. 


Farashin Dalar Amurka ya kai N515, hakan ya na nufin Naira ya rasa N5 a cikin sa’a 24. Kafin Laraba, an saida kowane Dalar Amurka ne a kan N510. 


Rahoton ya ce Nairar ta yi hobbasa ne a ranar 4 ga watan Agusta, lokacin da Dalar Amurka ta koma N506, kafin nan sai da aka saida Dala a kan N525. 


Tun bayan lokacin da ‘yan canji na Bureaux de Change suka daina samun kudi daga CBN, farashin Dalar yake ta yawo tsakanin N508 zuwa N510. 


Naira ta kara karfi a wajenmu - FMDQ FMDQ Group ta bayyana cewa Naira ta na kara daraja ne a wajenta, kudin gidan ya kara kima da 0.02% a hannun masu alaka da masu kasuwanci a ketare. 


Rahoton ya nuna cewa masu karbar Dala da sauran kudin kasar waje domin su shigo da kaya daga ketare sun saye kowane Dalar Amurka a jiya a kan N411. 


Alkuma sun tabbatar mana an samu raguwar masu fita fatauci a kasashen ketare a makon nan, abin da aka kashe ya ragu daga $590m zuwa $489m a jiya. 


Matakin da CBN ta dauka 


Naira ta yi raga-raga ne bayan matakin da babban bankin kasa na CBN, ya dauka a karshen watan Yuli, na hana saida wa ‘yan canji kudin kasashen waje. 


Godwin Emefiele ya bada sanarwar hana masu kasuwancin BDC kudin ketare, saboda ana hada-kai da su wajen yin ta’adi, aka koma ba bankuna kasonsu. 


Najeriya na fuskantar matsalar cin bashi An ji cewa Indiya da Najeriya suna cikin kasashen da su ka fi kowane yawon cin bashin kudi a Duniya. 


An fara tsoro kar bashi ya yi wa kasashen nan katutu. Sai dai duk da haka, gwamnatin Najeriya ba ta yarda cewa yawan bashi zai yi mata daurin goro ba 


Source: Legit

0 Response to "Duba yadda Darajar Naira ta qara sauka kasa, Yanzu farashin Dalar Amurka $1 yakai N515 a kasuwa, "

Post a Comment