--
Zan maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47 - Lauya

Zan maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47 - Lauya

>


Wani dan rajin kare hakkin dan adam, Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya yi barazanar maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu game da bayar da lasisin mallakar bindiga kirar AK-47 don kare kai.


Omirhobo a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Yulin 2021, ya bukaci shugaban da ya amince da mallakar bindigogi ga mutane don kare kansu, iyalai da dukiyoyinsu daga harin 'yan ta'adda masu rike da muggan makamai. 


Da yake magana da Daily Trust, lauyan ya ce a shirye yake ya kalubalanci shugaban a kotu kan wannan batun a cikin kwanaki masu zuwa. 


Ya ce: “Ni dan Najeriya ne mai kiyaye doka, a likitance kuma mai hankali. Ni mutum ne mai dabi'a mai kaifin hali kuma ba a taba tuhuma ta cikin shekaru biyar da suka gabata ba game da wani laifi da ya shafi tashin hankali ko barazana." 


Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito. 


Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar. 


Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020. 

0 Response to "Zan maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47 - Lauya"

Post a Comment