--
Daga Qarshe Sheikh Abduljabbar Kabara yayi wata magana Akan Muqabalar da Akayi Dashi Duba Abinda Yace>>>

Daga Qarshe Sheikh Abduljabbar Kabara yayi wata magana Akan Muqabalar da Akayi Dashi Duba Abinda Yace>>>

>


Sheikh Abduljabbar ya nemi afuwar al'ummar musulmi game da zargin batanci ga Annabi  (S)


Malamin ya bayyana hakan ne cikin wata sakon murya yana mai cewa ba a fahimce shi bane Abduljabbar ya ce idan har ya tabbata cewa abin da ya furta a karatunsa kirkira ya yi toh tabbas yana neman afuwa


kuma zai gaggauta tuba Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi al'ummar musulmi su yi masa afuwa game da kalaman batanci ga Annabi Muhammadu SAW da ake zarginsa da yi yana mai cewa 'ba a fahimce shi' bane, BBC ta ruwaito. 


An ji malaman cikin wani sakon sauti yana cewa: "Idan har wadannan kalamai daga ni suke, kirkirarsu na yi, ba su a litattafai toh lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni da na gaggauta tuba" 


Ya cigaba da cewa: "Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancen litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. 


Sai mu yi rokon Allah ya haska wa al'umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan karya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su." 


A hirar da ya yi da BBC, Abduljabbar ya jadada cewa yana neman afuwar wadanda ke ganin kalaman da ake cewa ya yi suna batanci ne ga Annabi a wajen fassara hadisan da aka gabatar a wurin mukabala. Kalaman malamin har yanzu na nuna cewa bai sauya abin da ya fada ba tunda farko. 


Ku saurari karin bayani .... 


Source: Legit 

0 Response to "Daga Qarshe Sheikh Abduljabbar Kabara yayi wata magana Akan Muqabalar da Akayi Dashi Duba Abinda Yace>>>"

Post a Comment